<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Knowles Shaw, George Austin Minor</author>
<hymn_number>335</hymn_number>
<title>Damuna Ta Faɗi, Ana Ta Yin Ruwa LW335</title>
<lyrics>[V1]
 1) Damuna ta faɗi, ana ta yin ruwa
 Daidai shukar iri, ƙasa ta yi kyau.
 Sai mu yi wa Yesu shukarsa a gona,
 Kada shi ya ga mai fasa aiki yau.

[V2]
 KORUS
 Farar zuciya, farar zuciya,
 Lalle za mu samu in kaka ta yi,
 Manyan dammuna, manyan dammuna,
 Lalle za mu samu in kaka ta yi.

[V3]
 2) Ko da rashin ruwa, ko da wani abu
 Wanda ya yiwu ya ƃata mana rai,
 Sai mu dinga noma, muna roƙon Allah,
 Kwana tashi, sai hatsi ya fid da kai
 Korus

[V4]
 3) &quot;Sai ku yi addu'a,&quot; in ji Almasihu,
 &quot;Sai ku roƙi wanda girbi nasa ne,
 Masu iya aikin girbi dai ya aiko
 Zuwa gonar hatsi, domin ya nuna!&quot;
 Korus</lyrics>
</song>